Hausa News : APC ta dare a jihar Zamfara


Bangarorin jam'iyyar APC biyu a jihar Zamfara na ikirarin korar manyan jam'iyyar a bangarorin da suke hamayya da su.
Bangaren da ke biyayya ga tsohon gwamnan jihar Abdulaziz Yari ya yi ikirarin korar Sanata Kabiru Marafa da tsohon mataimakin gwamna Ibrahim Wakkala.
Dayan bangaren mai biyayya ga Sanata Marafa ya bayar da sanarwar korar tsohon gwamnan Abdulaziz Yari da kuma wasu jiga-jigan jam'iyya a jihar.
Sai dai tsohon mataimakin gwamnan jihar Zamfarar Ibrahim Muhammad Wakkala ya ce bangaren Abdulaziz Yari ba shi da hujjar dakatar da shi da Kabiru Marafa bisa hujjar kai jam'iyya kara.
Asali ma, ya ce bangarensu bai taba kai jam'iyya kara ba tunda aka fara rikicin illa shiga shari'ar kawai.
Ya kuma ce kotu ta hana duka bangarorin fitowa su bayyana kansu a matsayin shugabannin jam'iyya.
"APC tana da bangarori guda biyu, akwai bangaren Abdulaziz Yari akwai kuma bangaren Kabiru Marafa kuma ko wannensu yana da shugabanni kuma ko wannensu ya yi zabe. An je kotu kuma ta dakatar da kowa daga fadin shi ne jagoran jam'iyya,"
"Don haka wace hujja suke da ita, ta dakatar da mu?" a cewarsa.
"Na yi imani uwar jam'iyya ta kasa za ta duba wannan abu, ta san wane ne ya kamata a kora, mu ko su" a cewarsa.
Ya kuma ce yana fata uwar jam'iyyar za ta yi adalci kuma ta yi abinda ya dace.
Sai dai sakataren walwala na jam'iyyar APC a matakin kasa, Ibrahim Masari ya ce ba ya tunanin rikicin ya kai da har uwar jam'iyyar za ta sa baki.
"Korafe-korafe wanda kusan ko wane gida akwai shi, na Zamfara ne dai ya yi kamari," in ji Masari.
Amma ya ce akwai kwamiti da uwar jam'iyya ta kafa don sauraren irin wadannan korafe-korafe na wasu 'yan jam'iyya da ake ganin sun yi wa jam'iyyar kafar ungulu kuma suna fata binciken kwamitin zai kunshi har da rikicin jihar Zamfara.
Ya ce daga nan ne jam'iyyar za ta san irin hukuncin da za ta dauka don ladaftar da masu irin wadannan laifuffukan.

Asalin Rikicin APC a Zamfara

Jam'iyyar APC a jihar Zamfara ta rabu gida biyu ne, wato bangaren gwamnan jihar mai ci Abdul'aziz Yari da kuma daya bangaren na Mataimakinsa da ministan tsaro da Sanata Marafa da Hon Jaji.
Rikicin na APC a Zamfara ya samo asali ne bayan da Gwamna Abdulaziz Yari ya sanar da goyon bayansa ga kwamishinansa na kudi, Alhaji Muktar Shehu Idris, a matsayin wanda zai gaje shi.
APC a Zamfara ta gaza gudanar da dukkanin zaben fitar da 'yan takararta na gwamna da na yan majalisar tarayya da na jiha.
Wannan ne ya sa wasu daga cikin masu sha'awar takarar gwamnan a jam'iyyar APC su takwas da suka hada da mataimakin gwamnan Ibrahim Wakalla da kuma Ministan tsaro Mansur Dan Ali suka hade kai domin yakar gwamnan na Zamfara.
Sau biyu ana shirya zaben fitar da gwanin a jihar, amma sai a soke saboda rikicin siyasa tsakanin bangarorin jam'iyyar a jihar.
Bangaren gwamnan jihar, ya fake ne da sakamakon wani hukuncin babbar kotun jihar a Gusau, inda alkalin kotun ya ce an yi zabe tare ba hukumar zaben kasar umurnin karbar sunayen 'yan takarar bangaren gwamna da ya yi ikirarin gudanar da zaben.
Hukuncin wata babbar kotun tarayya a Abuja, ya tabbatar da matsayin hukumar zaben kasar na haramta wa duk 'yan takarar jam'iyyar APC daga Zamfara shiga zabukan kasar da za a yi cikin watan gobe da na jibi.
Hukuncin ya ci karo da na kotun jihar karkashin mai shari'ah Muhammad Bello Shinkafi.
Sai dai mai shari'a Ijeoma Ojukwu ta kotun tarayya ta jaddada matsayin INEC inda ta ce jam'iyyun siyasa za su ci gaba da yin karan-tsaye ga ka'idojin zabe muddin suka kasa mutunta sharuddan da aka shata na jadawalin zabe.
Kotun ta ce hukuncin darasi ne ga sauran jami'yyun siyasa a nan gaba.
Bayan dage zaben 2019 ne wata kotu a Abuja ta ba hukumar zabe umurnin ta karbi 'yan takarar jam'iyyar APC, matakin da ya sa APC ta shiga zabukan 2019 a Zamfara.
Wata kotun daukaka kara a Sokoto ce kuma ta soke hukuncin umarnin da kotun Abuja ta bayar, inda kuma bangaren gwamnati ya daukaka kara zuwa kotun koli.
Kotun Koli ta soke zaben 'yan takarar jam'iyyar ta APC baki daya.
Babbar kotun kolin Najeriya ta ce jam'iyyar APC ba ta yi zabukan fitar da gwani ba, don haka jam'iyyar da take bin APC a yawan kuri'u ita ce ta lashe zabukan jihar da aka yi a watan Maris.
A wani zaman kotun da aka yi, an yanke hukuncin cewa jam'iyyar APC ba ta gudanar da sahihin zaben fidda gwani ba gabanin babban zaben shekarar 2019 a jihar.
Hukuncin kotun ya jaddada hukuncin da kotun daukaka kara a jihar Sokoto ta yanke, wadda ita ma ta yanke hukuncin cewa jam'iyyar APC ba ta gudanar da sahihin zaben fidda gwani ba a jihar.
Kotun kolin ta ce jam'iyyar ba ta da halaltattun 'yan takara don haka ba za ta iya kasancewa wadda ta lashe zabukan jihar ba.
Hakan na nufin APC ta rasa kujerar gwamna da dukkanin kujerun 'yan majalisar Tarayya da na jiha.

0 Comments